France-Turkiya

Fransa zata gyara dangantakarta da kasar Turkiya

dakarun daular ottomans tsaye bayan da suka rataye Arméniyawa da suka ci da yaki a garin  Alep a 1915.
dakarun daular ottomans tsaye bayan da suka rataye Arméniyawa da suka ci da yaki a garin Alep a 1915. AFP

Shugaba Francois Hollande, ya sha alwashin yin kokarin kyautata dangantakar da ke tsakanin Faransa da Turkiyya.

Talla

Kafafen yada labarum kasar Turkiyya sun rawaito Shugaba Abdullah Gul na bayyana cewa Shugaba Francois Hollande, wanda ke Magana yayin tattaunawar su a karon farko, yana cewa ya kamata a kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen 2, da a baya ta yi tsami.

Hollande ya kuma yi alkawarin bude sabon babin dangantaka tsakanin kasashen, da a baya ta sami koma baya sakamakon adawar da faransa ta nuna kan kan shigar Turkiyya kungiyar kasashen Turai.

Batun dokar nan da ke nuna laifi ne a ki amincewa da kisan kare dangin da aka yi wa Armeniyawa, a matsayin laifi ma ya kara takun saka tsakanin kasashen.

A watan Fabrairu wata kotun Faransa ta soke dokar, amma duk da haka ta jawo zanga zanga a Turkiyya da gargadin fansa daga hukumomin burnin Ankara.

Armeniyawa sun ce an hallaka musu dangin su kusan miliyon 1 da rabi karkarshin tsohuwar daular Ottoman tsakanin shekarun 1915-16, sai dai Turkiyya ta ce mutane dubu 500 ne suka mutu sakamakon yake yake da yunwa a lokacin yakin duniya na 1.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.