Faransa-Mali

Hollande ya yi tir da harin da aka kai wa Traore a Mali

Shugaban kasar Faransa  François Hollande,
Shugaban kasar Faransa François Hollande, REUTERS/Philippe Desmazes/

Shugaban Faransa Francois Hollande ya yi Allah waddai da harin da masu zanga zanga suka kai wa shugaban riko na kasar Mali, Dioncounda Traore, inda suka mi shi duka tare da neman shugaban ya yi murabus.

Talla

Lamarin ya zo ne kwana guda, bayan da wakilan kungiyar hadin kan tattalin arzikin yankin Afrika ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO suka kulla wata yajejeniya da sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hulan kasar.

Kamar yadda aka tsara yarjejejniyar, Traore zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya tsawon watanni 12, kafin ya mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.