Norway

Anders Behring Breivik wanda ya kashe mutane 77 a kasar Norway ya ce ya shiryawa kowane hukumci

Anders Behring Breivik, wanda ya hallaka mutane  77 a ranar 22 juli 2011 a Norway
Anders Behring Breivik, wanda ya hallaka mutane 77 a ranar 22 juli 2011 a Norway Reuters / Lise Aserud

Anders Behring Breivik, mutumin da ake shariarsa a kasar Norway saboda kashe mutane akalla 77 ha ka kawai, ya shaidawa kotun dake shariarsa cewa, komi ta fanjama fanjam, duk abinda kotu ta zartas akansa ya amince.Dan shekaru 33 Anders Behring Breivik ya fadawa kotu yau cewa, babu wani dalili da zai sa shi ya daukaka kara idan aka zartas masa da hukunci.