Libya-kotun duniya
Tsohin yan tawayen kasar Libiya sun hana a dauki dan marigayi Ma'amar Kadhafi zuwa Tripoli har sai an biyasu
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Babban jakadan kasar Libya a kotun kasa-da-kasa Ahmed al-Jehani yace matsala aka samu a Libya wajen jinkirin biyan hakkokin tsoffin ‘yan tawaye, yasa aka kasa kai fitaccen dan marigayi Moammar Gaddafi, wato Seif al-Islam , zuwa Tripoli daga inda ake tsare dashi. Acewar jakadan ana bukatar kudaden da suka kai kudin Amirka Dollar $1.36 domin biyan tsoffin ‘yan tawayen hakkokin su.Shidai fitaccen dan marigayi Moammar Gaddafi Seif al-Islam, 39 ana tsare dashi ne a gidan yari dake garin Zintan mai kimanin kilomita 180 kudu maso yammacin birnin Tripoli