Italiya

Mutane sama da 10 ne suka mutu a wata sabuwar girgizar kasar da ta wakana a kasar Italiya

Les secours dans les décombres à Medolla, dans la province de Modène, le 29 mai 2012.
Les secours dans les décombres à Medolla, dans la province de Modène, le 29 mai 2012. REUTERS/Giorgio Benvenuti

Wata sabuwar girgizar kasa da ta shafi yankin arewa maso gabashin kasar Italiya ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 10 tare da jikkata wasu da dama, kwanaki 9 bayan abkuwar girgizar kasar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 6, tare da raba wasu dubbai da mahallansu a wannan yanki.

Talla

Jaridar Gazzetta di Modena, da ake bugawa a yankin Emilie-Romagne inda girgizar kasar ta faru ta bayyana cewa, mutane 12 ne suka rasa rayukansu.

Cibiyar binciken ma’adanai da kuma duwatsu masu aman Wuta ta kasar Italiya (INGV) ta ce, sabuwar girgizar kasar da ta wakana da misalin karfe 7:00 na safiyar yau talata a gogon GMT da cewa, ta kai karfin maki 5,8 bisa ma’aunin Rishta, kuma ta faru ne da zurfin kilo mita 5 zuwa 10 a karkashin kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.