Rasha

Putin zai kai ziyara Faransa da Jamus

Shugaban Rasha Vladmir Putin da Fira Minista  Dimitry Medvedev
Shugaban Rasha Vladmir Putin da Fira Minista Dimitry Medvedev Reuters

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, zai kai ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje, inda zai ziyarci kasashen Belarus, Jamus da Faransa a cikin wannan mako, don ganawa da shugaba Alexander Lukashenko da Angela Merkel da Francois Hollande. Wannan ziyara zata bude wani babin dawowar Putin siyasar duniya, bayan dawowa shugabancin kasar, inda ake saran zai taka rawa wajen warware matsalar siyasar Syria.