Afrika-Malte-bakin haure

Shugaban Tsibirin Malta ya gargadi kasashen turai kan kwararar bakin haure

bakin haure a tsibirin Malta
bakin haure a tsibirin Malta © Reuters/Darrin Zammit Lupi

Shugaban kasar tsibirin Malta George Abela ya gargadi kungiyar tarayyar Turai, kan ta dauki matakan da suka dace domin kawo karshen kwararar bakin haure daga yankin arewacin nahiyar Afrika, al’amarin da addabar wannan dan karamin tsibiri dake Tukun Mediterraniya.  

Talla

Shugaban Tsibirin na Malta M. Abela ya bayyana cewa ala’amurra basu daidaita ba a kasashen Arewacin Afrika, kuma wannan zai ci gaba da shafar tsibirin nasu, M. Abela na tsokaci ne kan rikicin siyasar baya bayan nan da ya shafi kasashen arewacin Afrika da suka hada da Tunisiya Libiya da kuma Masar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.