Turai

Matasan kasashen turai sun rage shan miyagun kwayoyi sun koma zukar taba sigari

REUTERS/Marcelo del Pozo

Wani bincike da wata kungiya dake sa idanu kan shan miyagun kwayoyi a kasashen Turai ta gudanar na cewa yawan matasa dake shan miyagun kwayoyi a kasashen Turai na raguwa, amma mafi yawa na komawa zukar taba sigari ne.  

Talla

Kungiyar mai mazaunin ta a Lisbon tace tayi nazarin ta a kasashe 36, inda ta fahimci cewa matasa dalibai masu shekaru tsakanin 15-16 sun rage muamulla da miyagun kwayoyi.

Binciken da aka bayan na daga cikin irin nasarori da ake samu na yaki da shan taba sigari, kasancewar yau aka ware domin bukin juyowar ranar yaki da shan taba sigari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.