Faransa-Jamus

Faransa da Jamus sun yi bukin shekaru 50 da dakatar da yaki

Shugabannin Faransa da Jamus suna sumbantar juna
Shugabannin Faransa da Jamus suna sumbantar juna REUTERS/Jacky Naegelen

A dai dai lokacin da kasashen Faransa da Jamus ke kokarin shawo kan matsalar da ta dabaibaye kudin EURO, kasashen 2 sun yi bukin cikar shekaru 50 da kawo karshen yakin da suka gwabza tsakanin su. An fara bukin ne da addu’oi a majami’ar garin Rheims, inda shugaba Farncois Hollande da shugabar gwamnatin Jamus Agela Markel suka halarta.Shugabannin 2 sun ce yanzu abu mafi muhimmanci shine hade kan kasashen nahiyar Turai.Shuagabannin 2 sun sunbanci juna a kumatu, alamar da ke nuna gaisuwa tsakanin su, da kira juna sunan abota, maimakon lakanin da a baya suke wa juna a hukunce, sai dai duk da haka lalata kaburburan sojan Jamus 51 da aka yi a garin na Rheims da ke arewacin Faransa ya rage wa bukin armashi.Shugaba Francois Hollande bai yi wata wata ba wajen kokarin wanke Faransa daga duk wani zargi kan batun, inda ya shaida wa Angela Markel da ma sauran mahalarta bukin cewa ba wani abu da zai iya canza dagantakar da ke tsakanin kasashen 2.Ministan harkokin cikin gidan Faransa Manuel Valls ya yi Allah wadi da lalata kabururan sojojin na jamus, inda yace za a yi bincike don gano wadanda suka yi aika aikar.