Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya ziyarci yankunan da ambaliyar Ruwa ta shafa a kasar sa.

Shugaban Rasha Vladmir Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ziyarci Yankin kudancin kasar, dan ganewa idansa yadda ambaliyar ruwa yayi ta’adi, inda akalla mutane 171 aka tabbatar da mutuwar su a hadarin.  

Talla

Vladimir Putin yace zai gudanar ta yiyara ta musamman saboda kafafen watsa labarai na ta yada jita-jitar cewar ba’ayi cikakken gargadi akan aukuwar wannan bala’in ba.

Koma a ambaliyar ruwan da aka sama a yankin Krasnodar ta hallaka akalla mutane da dama a ranar 7 ga watan Yulin daya gabata, tareda akuma lalata fiyeda kayayyaki 3000.

Shugaba Putins yace mutane nata kururuta cewar ba’ayi kashedi kan wannan matsalar ba, duk da cewar gwamnatin data gabata tayi irin nata kokari.

Amma duk da haka Putin yayi gargadi da kakkausar murya cewar lallaine jami’an hukumarsa su hakikance namijin kokarin da sukayi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.