Turai-Isra'ila

Kasashen Turai za su inganta hulda da Isra’ila

Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Hillary Clinton tare da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Hillary Clinton tare da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Reuters

Wata Majiyar Diflomasiya tace kasashen Turai za su inganta hulda da kasar Isra’ila bayan a kwanan baya kasashen sun yi Allah Waddai da tsare tsaren Isra’ila. Ana sa ran kasashen za su amince da sabuwar dangantar tsakaninsu da Isra’ila a taron da za su gudanar da birnin Brussels a gobe Talata.

Talla

A wata sanarwa da kasashen suka fitar a watan Mayu ministocin harakokin wajen kasashen kungiyar 27 sun yi kakkausar suka ga Isra’ila akan yadda ta ke cin zarafin Falesdinawa.

Majiyar tace kasashen Turai za su inganta huldar kasuwanci ne da Isra’ila da suka kunshi huldar Sufuri da Makamashi da sauran fannoni kimanin 60.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.