Sweden-Australia

Australia tace zai yi wahala Sweden ta mika Assange zuwa Amurka

Shugaban Shafin kwarmata bayanan Siri na WikiLeaks,  Julian Assange a kofar shiga Ofishin jekadancin Ecuador inda ya samu mafaka a Birtaniya
Shugaban Shafin kwarmata bayanan Siri na WikiLeaks, Julian Assange a kofar shiga Ofishin jekadancin Ecuador inda ya samu mafaka a Birtaniya Reuters

Gwamnatin kasar Australia tace zai yi wahala Sweden ta mika mutumin da ya kirkiro shafin kwarmata bayanai na WikiLeaks, Julian Assange zuwa Amurka, indan akwai yiwuwar yanke mi shi hukunci kisa, ko gurfanar da shi a kotun soja.Ministan harkokin wajen Australiya Bob Carr yace kasar shi ba za ta tsoma baki ga lamarin da ke faruwa a wata kasa ba, amma kuma gwamnatin Sweden tace zai yi wuya ta mika shi Amurka.

Talla

Magoya bayan Assange dan kasar Australia suna ganin idan har aka mika shi Sweden, hukumomin kasar za su iya tura shi Amurka don a yanke ma shi hukunci kan zargin leken asiri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.