Faransa da Spain sun nemi takaita kudaden rance
Wallafawa ranar:
Kasashen Faransa da Spain, sun hada Kai, domin yin kira ga kasashe masu amfani da kudin Euro don daukar muhimmin matakin takaita adadin kudin da ake iya rance, abinda suke ganin ya kai Spain ga neman madafar shawo kan matsalar tattalin arzikinta.
Shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana cewa a ran 29 ga watan Yuni ne babban Bankin yankin kungiyar Tarayyar Turai ya amince da matakan da za su bai wa babban bankin damar shiga ga wani hali.
Yace yanzu ya ragewa babban bankin akan ya aiwatar da shirin gwargwadon halinsa, sai dai yace yanason ya tunatar da daukacin kasashen yankin cewa daga cikin manufofin babban bankin akwai daidaita farashin kaya, amma kuma akwai zancen tsare-tsaren tafiyar da al’amurran kudade tsakanin kasashen.
Daukacin kasashen Turai dai na goyon bayan daukaka darajar kudin euro, amma shugaban gwamnatin kasar Spain Mariano Rajoy yace lallai ne gare su su shawo kan matsalar da suke fama da ita, domin a yayin da wasu kasashen ke tafiyar da al’amurran gudanarwarsu da tsada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu