Jamus

Jamus ta yi gargadi akan dogaro akan bankin nahiyar turai na ECB

Ministan kudin kasar Jamus, wolfgang Schaeuble, ya yi gargadi akan saka dukkan tsammani akan bankin nahiyar Turai, ECB, a kokarin da ake yi na samo maslahar matsalar tabarbarewar tattalin arzikin yankin.

Bankin Tarayyar Turai, ECB
Bankin Tarayyar Turai, ECB Reuters/Ralph Orlowski
Talla

“Dole ne mu yi takatsantsan kar mu saka dogaro gaba daya (akan ECB).” Inji Schaeuble, a wata hira da ya yi da gidan Radiyon Al’umar Deutschlandfunk.

Gwamnatin Jamus na ganin cewa bai kamata tsare-tsaren manufofi tattalin arziki ya zamanto hanyar samarwa kasashe kudade ba.

Kasuwanni da dama a nahiyar ta Turai na ta kallon bankin na ECB a matsayin wata kafa da su ke zaton za su sami mafita daga matsalar tattalin arziki.

Sai dai shugaban babban bankin kasar Jamus da kuma kwamitin da ke kula da bankin na ECB sun ce basu amince da yin wannan tsari ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI