Italiya

Monti zai karbi bakuncin Hollande akan yankin kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro

Firaministan kasar Italiya, Mario Monti, zai karbi bakuncin Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, inda za su tattauna akan matsalar tattalin arziki da yankin kasashen nahiyar turai masu amfani da kudin bai daya na Euro ke fama da shi.

Shugaban kasar Italiya, Mario Monti
Shugaban kasar Italiya, Mario Monti Reuters/Max Rossi
Talla

Wani babban jami’in kasar Faransa, ya bayyanawa, Kamfanin Dillancin labaran Faransa na AFP, cewa za su tattauna ne akan yadda za a yi amfani da matakan da za su magance matsalar.

Haka kuma, an rawaito cewa za su tattauna akan sabbin batutuwa da su ka taso su ka kuma shafi tattalin arzikin kasashen.

AFP ta kuma rawaito cewa, za su gana a kan yadda za a habaka kusanci akan tattalin arzikin kasashe ta yadda za a fitar da wani shirin da zai saka ido akan bankuna nan daga nan zuwa karshen shekarar nan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI