Jamus

Girka ba za ta samu taimako na uku ba, inji Jamus

Ministan kudin kasar Jamus, Wolfgang Schaeuble, ya ce kasar Girka ba za ta samu taimakon ceto tattalin arzikinta ba a karo na uku, sai dai ya jaddada cewa, kasar ta Girka za ta cigaba da kasancewa a yankin na kasashen da ke amfani da kudin bai daya na euro. 

Ministan kudin kasar Jamus, Wolfgang Schaeuble
Ministan kudin kasar Jamus, Wolfgang Schaeuble REUTERS/Thomas Peter
Talla

Schaeuble ya fadi hakan ne a wata hira da gidan Radiyon kasar Jamus ta yi inda ya ce kudaden da ake bin kasar ta girka ya yi yawa.

A wataN Mayun shekarar 2010 ne kasar ta Girka ta zamanto kasa ta farko a yankin da ta samu taimakon kudin euro biliyan 110 da sharadin cewa za ta dauki matakan tsuke bakin aljihunta.

A watan Oktoba 2011 kuma, aka kara ba kasar ta Girka kudin euro biliyan 130 aka kuma yafe mata bashin kudin euro biliyan 100.

Amma a yanzu haka kasar na bukatar ta biya bukatin masu bata bashi wadanda akewa lakabi da “Troika” inda ta ke bukatar wasu kudade.

“yanzu dole ne sai Troika sun bamu rahoto a watan Oktoba” inji Schaeuble.

Ya kuma kara da cewa dole ne kasar ta Girka ta cigaba da kasancewa a cikin kasashe 17 dake amfani da kudin na euro, inda ya kara da cewa, “babu mafita ga kasar ta Girka.”

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI