Babu siyasa a mutuwar Magnitsky, inji Putin
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu batun siyasa cikin mutuwar Lauyan nan, Sergie Magnitsky, wanda ya a mutu a gidan yari a shekarar 2009. “Ina tabbatar muku cewa babu siyasa a cikin mutuwar,” inji Putin, a hirarsa da ya yi da jaridar Russia Today.
Putin ya kuma dauki alwashin daukan tsatstsauran mataki akan duk kasashen yammcin duniya da su ka alakanta kisan ga jami’ansa.
An dai tsare Magnitsky, dan shekaru 37, a gidan yari, bayan ya yi zargi cewa jami’an gwamnati na da hanu a cikin mallake wani kamfanin maigidansa da kuma yin badakalar daruruwan miliyoyi na dalar Amurka.
Ya kuma mutu ne snadiyar rashin samun kula daga likitoci da kuma zargi cewa an azabtar da shi.
Lamarin dai ya jawo hankalin kasashen duniya inda aka fitar da jerin sunaye daga kasashen yammacin duniya wadanda ke da hanu a mutuwar ta Magnitsky.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu