Fransa-Najeriya

kotu a Fransa taci tarar wani kamfanin kasar kan bada cin hanci ya karbi kwangila a Najeriya

Wata kotu a kasar Faransa ta samu wani kamfanin kasar mai suna Safran, da laifin bayar da cin hanci ga jami’an Najeriya domin samun kwangilar samar da katin shedar zama dan kasa. Shekaru Tara bayan samar da katin shedar da aka kashe makudan daloli a kai, Kotun ta ci tarar kamfanin na Safran Dalar Amruka 600,000. Jean Jacques Terray na kungiyar Transferency a Faransa yace wannan ne karo na farko da aka samu wani kamfanin Faransa da karbar cin hanci. 

unknozn