Faransa

Mutane hudu sun mutu a kasar Faransa

Shugaban kasara Faransa, François Hollande
Shugaban kasara Faransa, François Hollande Reuters

A yankin Alps da ke gabashin Faransa, an samu mutuwar mutane hudu da suka hada da wata yarinya karama, a cikin wata mota kirar BMW da aka harbe da bindiga. ‘Yan Sandan Faransa sun ce sun gano an yi rigister motar ne a Birtaniya, amma har yanzu suna ci gaba da binciken gano wadanda al’amarin ya shafa.  

Talla

Wani mutum da ake tunanin shi ma harbin ya ritsa da shi a lokacin day a ke ratsawa akan keke ya mutu a harin.
 

‘Yar uwar yarinyar da aka kashe an sameta ne a gefen wata mota an harbeta kuma tana cikin wani halin ni ‘yasu bayan an garzaya da ita zuwa asibiti a cikin jirgi sama mai saukar angulu.
 

Jami’in da ke binciken kisan, Eric Maillud, ya ce wata ‘yar shekaru hudu ta tsallake rijiya da baya a harin.

A cewarsa, ta buya ne a karkashin gawawwakin da aka kashe har na tsawon sa’oi takwas inda ta kame ba tare da ta motsa ba.

Har yanzu dai a cewar rahotanni ba a gane ko su waye ba wadanda su ka mutu a harin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.