Birtaniya ta nemi Kungiyar Tarayyar Turai ta tsaurara takunkumin kasar Iran
Sakataren harkokin wajen Kasar Birtaniya, William Hague, ya yi kira ga Kungiyar Tarayyar Turai da ta kara himma wajen tsaurara matakan kakabawa kasar Iran takunkumi, saboda sarrafa sanadrin Nukiliay da kasar ke yi. “Ya na da matukar muhimmanci a kara tsaurara matakan da aka dauka na kakabawa kasar Iran takunkumi,” inji Hague
Wallafawa ranar:
Hague ya yi kiran ne a lokacin daya ke kan hanyarsa ta haduwa da takwarorinsa a taron kasashen nahiyar Turai su 26, inda za su tattauna akan batutuwa da dama da su ka hada da batun rikicin Syria a Cyprus.
A watan Yuli ne aka kakabawa Iran takunkumi akan manta a kokarin rage yawan man da kasar ta ke sayarwa a kasuwar duniya.
Ana dai sa ran taron zai bada bayanai akan irin tattaunawa da aka kwashe watanni ana yi da kasar ta Iran.
Kasar Birtaniya dai za ta nemi kungiyar EU da ta fidda sabbin takunkumi wanda zai shafi bagaren makamashi da kuma hada hadar kasuwancin kasar ta Iran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu