Amurka

Dankon zumunci Amurka da Rasha na nan daram – Amurka

Shugaban kasar Amurka, barack Obama
Shugaban kasar Amurka, barack Obama AFP PHOTO / Saul LOEB

Dangantakar da ke tsakanin kasar Amurka da kasar Rasha na nan daram bayan sun karfafa dankon zumunci da ke tsakaninsu, a cewar wani babban jami’in Amurka.

Talla

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama dai ya yi kokarin karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu bayan ya hau karagar mulki a shekarar 2009.

Obama da takwaransa, Vladimir Putin, sau daya tak su ka hadu bayan an sake zaben da Putin ya lashe, inda shugabannin su ka samu sabani a tsakaninsu musamman akan batun rikicin Syria da Rasha ke bin goyon bayan gwamnatin kasar ta Syria.

Putin dai na zargin fadar White House da goyon bayan masu bore akan gwamnatinsa lokacin zaben kasar ta Rasha.
 

An dai tambayin shi jami’in na kasar Amurka yaya dangantakar kasashen biyu ta ke, sai ya kada baki ya ce “tan an da kyau.”

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.