Habasha

Habasha ta saki ‘Yan jaridun kasar Sweden

Tutar kasar Sweden
Tutar kasar Sweden www.google.fr

Gwamnatin kasar Habasha, ta saki ‘Yan jaridun kasar Sweden su biyu wadanda aka kamasu a yankin ‘Yan tawaye da ke Ogaden. An samu ‘Yan jaridun da laifin taimakawa ‘Yan tawayen aka kuma yanke musu hukuncin zaman gidan ya na tsawon shekaru 11. 

Talla

Kamfanin Dillancin labaran kasar Faransa na AFP, ya rawaito cewa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Dina Mufti, ya bayyana cewa, tsohon Firaministan kasar, Meles Zenawi, ya tun kan ya rasu ya ce a sakesu a matsayin yafiya.

Wani babban jami’in kasar ta Habasha ya ce yafiyar da akawa ‘Yan jaridun na daga cikin yafiyar da akan yi ga masu laifi da ke gidan kaso a lokaci lokaci.

A watan Yulin bara ne aka kama Martin Schibbye da mai daukan hotonsa, Johan Persson a kasar ta Habasha.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.