Faransa

Hollande ya yi alkwalin bunkasa tattalin arzikin Faransa

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande, ya yi alkawarin samar da euro Biliyan 30 ta hanyar tara sabbin kudadenn haraji daga attajirai domin cike gibin kasafin kudi a cikin shekaru biyu. Shugaban yana kokarin cika alkawlain da ya dauka ne na samar da kashi 75 daga kudaden haraji a lokacin da ya key akin neman zaben shi.

Shugaban kasar Faransa François Hollande, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gidan Telebijin
Shugaban kasar Faransa François Hollande, a lokacin da yake gabatar da jawabi a gidan Telebijin Reprodução
Talla

A lokacin da shugaban ya ke kare gwamnatinsa daga zargin jan kafa waje kin daukar matakan da suka dace, wanda kuma farin jininsa ke ci gaba da raguwa, yace babu gudu babu ja da baya wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Shugaban yace zai samar da euro Biliyan 10 daga harajin gidaje, tare da samar da Biliyan 10 daga kasuwanni, da wasu Biliyan 10 daga rage kashe kudaden gwamnati.

Shugaban yace Burin shi ne ceto tattalin arzikin kasar Faransa, nan da shekaru shekaru biyu domin cim ma biyan bukatun Faransawa, da samar da ayyukan yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI