Spain-Euro

Spain ta yi watsi da sharuddan bashin Turai

Firaminsitan kasar Spain, Mariano Rajoy yace ba zai amince da sharadodin bada rance da kasashen waje suka sanyawa kasar ba, duk da ya ke suna bukatar tallafi. Yayin da ya ke hirarsa ta farko a Talabijin, Rajoy yace ya zuwa yanzu, babu wani shiri na karbar tallafin.

Angela Merkel Shugabar gwamnatin Jamus da Firaministan Spain Mariano Rajoy, a lokacin da suke ganawa a birnin Madrid
Angela Merkel Shugabar gwamnatin Jamus da Firaministan Spain Mariano Rajoy, a lokacin da suke ganawa a birnin Madrid REUTERS/Andrea Comas
Talla

A makon jiya, shugaban Bankin kasasen Turai ya bayyana wani shiri na saye kadarorin kasashen euro da ke fama da dimbin basuka, kafin a basu tallafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI