Faransa

‘Yan sandan Faransa na tuhumar tsohon Firaminista Villepin

Tsohon Firaministan kasar Faransa, Dominique de Villepin
Tsohon Firaministan kasar Faransa, Dominique de Villepin REUTERS/Charles Platiau

‘Yan sandan kasar Faransa na tuhumar tsohon Firaministan kasar, Dominique de Villepin akan wata badakala da aka yi akan wani Otel din abokinsa.Wata majiya mai karfi ta tabbatarwa da Kamfanin Dillancin labaran Faransa na AFP, cewa ana tuhumar Villepin ne akan Otel wanda ake kira Relais & Chateaux wanda mai Otel, Regis Bulot ake zargin da yin wata almundahana. 

Talla

Ana dai zargin cewa, Villepin a shekarar 2011 ya buga wayar talho wacce ‘Yan sanda suka bi diddigi, inda aka ji shi yana cika bakin cewa ya taimaka wajen hana Otel din bawa ‘Yan sanda hadin kai a lokacin wani bincike da ake gudanarwa.

Villepin, wanda aka fi tuna shi da jagorantar yakin da yayi akan kasar Iraq a dandalin Majalisar Dinkin Duniya, ya dai musanta cewa yana da hanu akan zargin.

A watan Satumba, wani Lauya na hanun daman tsohon shugaban kasar, Nicolas Sarkozy ya ce da hanun Villepin a wata badakala da aka yin a wasu kudade masu yawa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.