Jamus

Kotun Jamus ta yi watsi da bukatar dakile shirin samar da asusun Turai

Shugabar gwamnatin Jamus Chancellor Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Chancellor Angela Merkel REUTERS/Fabrizio Bensch

Kotun Kolin kasar Jamus ta yi watsi da bukatar da wasu suka gabatar, na sanya shinge ga shirin kafa asusun ko ta kwana na kungiyar kasashen Turai.Masu adawa da shirin kafa asusun ne suka shigar da karar, a gaban kotun fassarra kundin tsarin mulkin kasar ta Jamus, inda suke cewa, asusun zai tilastawa Jamus sanya kudadenta dan ceto kasashen Turai da ke fama da matsalar bashi

Talla

Wannan dai ba karamar nasara bace ga masu neman ganin ci gaba da hadin kan kasashen Turai.

An dai fada cikin fargaba kafin hukuncin, inda ake tsoron cewar amincewa da karar na iya jefa daukacin kasashen Turai da ma kasuwannin duniya cikin halin kakanikayi.

Hukuncin kotun ya bai wa shugaban kasar Jamus, Joachim Gauk damar sanya hannu kan kudirin dokar amincewa da asusun.

Ganin yadda Jamus zata bayar da kashi 27 na kudaden da za’a sanya a asusun mai kunshe da euro Biliyan 500, ya zama dole ga ‘Yan kasar su amince da shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI