Faransa

Minista ya nemi ci gaba da wasan kaho a Faransa

Ministan Harkokin cikin gidan Faransa, Manuel Vals, ya kare wasan hawan kaho da ake yi a kasar, yayin da kotun fassara kundin tsarin mulki ke kokarin haramta wasannin. Ministan wanda aka Haifa a kasar Spain, inda hawan kaho ya zama jiki, yace wasa ne da ya riga ya zama al’ada a gare su, saboda haka haramta shi ba zai yi musu dadi ba.

Wani hoton takarda da ke dauke da bayanin neman haramta wasan kaho
Wani hoton takarda da ke dauke da bayanin neman haramta wasan kaho Photo: Reuters
Talla

‘Yan rajin kare hakkin dabbobi ne suka bukaci haramta wasa na hawan kaho saboda hadarin da ke cikin wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI