Kamfanin Jamus ya takaita shiga da maganin da ya yi sanadiyar mutuwar Michael Jackson
Kungiyar sarrafa magunguna na Fresenius da ke kasar Jamus, y ace ya takaita shigar da kwayar Propofol wacce ta yi sanadiyar mutuwar shahararren Dan wakan Kasar Amurkan nan, Michael Jackson.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yanke hukuncin yin hakan a cewar mai Magana da yawun Kamfanin, a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labaran AFP, ya biyo bayan sanarwa da wata Jiha a kasar Amurka ta yi na cewa za ta yi amfani da kwayar wajen aiwatar da wadanda aka yanke musu hukuncin kisa.
Kamfanin na Fresenius ya rage shigowa da kwayar daga kashi 30 zuwa kasa da kashi 15 a yunkurin da ake yin a takaita amfani da maganin.
Haka kuma kamfanonin da za su dimga shigowa da maganin sai sun yi alkawarin ba za su aika da maganin zuwa gidan yari ba, ko kuma zuwa ga hukumomin gidan yarin.
Ita dai wannan kwaya ta Propofol, it ace sanadiyar mutuwar Jackson a watan Yunin shekarar 2009 bayan ya sha ta fiye da kima, kuma a watan Mayu ne Jihar Missouri t ace za ta yi amfani da maganin wajen zartar da hukuncin kisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu