Faransa

Faransa ta tsaurara matakan tsaro a ofisoshin jakadancinta na ketare

Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Laurent Fabius
Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Laurent Fabius Reuters/路透社

Gwamnatin Kasar Faransa na cigaba da daukar matakan tsaro a ofisoshin Jakadancin ta dake kasashe 20 na duniya, saboda tsoron kai musu hari, sakamakon wallafa wasu hotuna da wata Mujallar kasar ta yi, inda ta danganta su da Manzan Allah, wanda tsira da amincin Allah suka tabbata a gare shi.

Talla

Daukar wanna mataki ya biyo bayan kunnen uwar shegu da Mujallar Charlie Hebdo ta yi, na kaucewa buga wadanan hotuna, wadanda suka ci zarafin addinin Islama da kuma Musulmin duniya.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya ce za’a rufe ofisoshin Jakadancin Faransa da makarantu ranar juma’a a kasashen Musulmi 20, dan kaucewa wadanda zasu gudanar da zanga zanga a ranar.

Ministan ya kara da cewa, yana fargaban abinda zai biyo baya, ganin cewar tuni an harzuka Musulmin duniya da fim din da akayi a Amurka, wanda aka sanya shi a yanar gizo.

Tuni aka girke Yan Sanda a ofishin Mujallar dake birnin Paris, dan magance duk wata barazana.

Firaministan kasar, Jean Marc Ayrault, ya ce duk wadanda basu ji dadin abinda mujallar tayi ba, na iya zuwa kotu don a bi masa kadi.

Shugabanin al’ummar Musulmin dake Faransa, sun yi Allah wadai da mujallar, inda suka bukaci kwantar da hankali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI