Kotun Faransa ta haramta buga hotunan matar Yarima Williams
Wata Kotu a kasar Faransa, ta haramta buga hotunan matar Yarima Williams, da kuma rarraba su, kana kuma ta umurci mika mata hotunan cikin sa’oi 24, sakamakon karar da gidan Sarautar Britaniya suka yi. Umurnin kotun ya ce, duk wani yunkuri na buga hotunan, ko kuma sanya su a shafin yanar gizo, na iya haifar da tarar euro 10,000.
Wallafawa ranar:
A cewar kotun, hotunan sun ketara sirrin Yarima da matarsa, inda kuma aka daukesu, za su iya tunanin su kadai ne a wurin.
Idan dai ba’a manta ba, Mujallar Closer ta buga wasu daga cikin hotunan Catherine William ba tare da riga ba, wadanda aka dauka lokacin da suka je hutu a Faransa.
Fadar Sarauniyar ya bayyana farin cikin sa da umurnin.
A yanzu haka kuma Yarima Williams dad a matarsa Catherine sun dauki hanyarsu ta komawa gida bayan wannan nasara da su ka samu a kotun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu