Amurka

Babban Bankin Amruka zai rage ma'aikata

Babban Bankin kasar Amurka na shirin rage ma’aikata dubu 16 a wani bangare na sake daidaita al’amuran gudanarwar Bankin a wannan shekara ta 2012.Hukumar gudanarwar Bankin ce ta sanar da haka tareda bayyana shirin a matsayin Dabara.  

La Réserve fédérale américaine, à Washington, le 22 août 2012.
La Réserve fédérale américaine, à Washington, le 22 août 2012. REUTERS/Larry Downing
Talla

Wannan matakin dai zai ragewa Bankin matsayin kasancewa Bankin da yafi kowane yawan ma’aikata a kasar ta Amurka.

A wani labari da Mujallar Wall Street Journal ta buga a yau Alhamis, wannan matakin na Babban Bankin, zai rage yawan ma’aikatansa zuwa dubu 260, adadin da ya kasance mafi karanci tun shekarar 2008.

Rage yawan ma’aikatan dai, wata Dabara ce da Bankin ya fito da ita domin hangen yadda Bankin zai kara inganci, tare da rage Dawainiya.

Mafi yawancin ma’aikatan da za’a rage dai, na daga bangaren Bankuna masu kula da Hidima ne, inda Bankin zai rufe wasu sassan sa.

Yanzu haka dai babban Bankin ya fara kakkafa cibiyoyin amfani da Katin daukar kudi na tafi da Gidanka wato’ Credit Card, da Sassan Inshora, da dai sauran fasalce fasalce, tareda rage yawan kadarorinsa zuwa kashi 7, na kwatankwacin Dollar Trillion 2.16 kenan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI