Italiya

Kotun Italiya ta tabbatar da hukunci kan ‘Yan kungiyar CIA

Wata babbar kotun kasar Italiya ta tabbatar da hukunci kan wasu jamian Kungiyar CIA saboda sace wani hamshakin Malamin Islama Dan kasar Masar a shekara ta 2003 a birnin Milan. Kotun ta kuma umarci a sake shariar wasu ‘Yan kasar Italian biyar da ake zargi da hannu wajen sace Malamin, Osama Mustapha Hassan da aka fi sani da Abu Omar.  

Tutar kasar Italiya
Tutar kasar Italiya wikimedia.org
Talla

Su dai jamian na CIA ana shari’ar sune ba tare da suna gaban kotu ba, a shari’ar da ake ganin babba ce sosai data shafi halaccin kasar Amurka wajen sa jami’an, ta su tatsi bayanai daga bakin wadanda suke zargi masu kishin Islama ne, gameda harin da aka kaiwa Amurka na 11. Ga watan Satambar shekara 2001.

Su dai jamian na CIA a shekara ta 2009 aka zartas masu da dauri na tsakanin shekaru 5-8 a gidan maza, sannan sai a watan 12 na shekara ta 2010 bayan daukaka kara aka kara wa’adin hukuncin zuwa zama gidan yari na shekaru tsakanin 7-9, sannan kuma su biya Malamin diyya.

Dukkan su jamian na CIA na da ‘Yancin su, yanzu amma kuma muddin suka tsoma kafarsu cikin Turai ana iya kama su.

Shi dai wannan Malami na samun mafaka ne a Italia alokacin, aka kama shi a 2003, aka garzaya dashi sansanin Sojan Amurka da ke Jamus, kafin su tattara shi zuwa Alkahira, inda ya ce an tozartashi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI