Monti ya yi kira ga Girka da ta cigaba da daukan matakan shawo matsalolin arzikinta
Firaministan kasar Italiya, Mario Monti, ya yi kira ga kasar Girka da ta cigaba da aiwatar da matakan da ta ke dauka na ganin cewa ta shawo kan matsalolin da ke addabar tattalin arzikinta. Monti ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke ganawa da takwaransa, Antonis Samaras a birnin Rome.
Wallafawa ranar:
Monti dai har ila yau zai gana da takwarorinsa na kasashen Spain da Ireland, wato Mario Rayjoy da Enda Kenny.
Shugabannin kasashen yankin masu amfani da kudin Euro na wani taro ne a birnin Rome na Centrist Democrat International inda ake sa ran zasu gabatar da jawabai.
Monti ya kuma yaba da irin ayyukan da Samaras ke gudanarwa, inda ya kara mai kwarin gwiwa da ya cigaba da ayyukan da yake yi.
Shugaban na Italiya dai ya sanar da koma bayan tattalin arzikin kasarsa kamar yadda aka yi hasashe daga kashi 2.4 a wannan shekara zuwa 0.2 a shekara mai zuwa, sai dai ya ce kasarsa ta Italiya ba ta bukatar a cetota.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu