Rasha

Suu Kyi ta yi kira ga Rasha da ta sake ‘Yan kungiyar Pussy Riot

Aung San Suu Kyi
Aung San Suu Kyi Reuters/Zoe Zeya Tun

Mai fafutukar wanzar da mulkin demokradiya, ‘Yar kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi ta yi kira ga hukumomin kasar Rasha da su sako ‘Yan kungiyar waka nan na Pussy Riot, wanda aka kulle su a watan da ya gabata. Su Kyi, wacce ta shafe shekaru 15 a daurin talala, ta nemi hukumomin kasar Rasha da su yi maza maza su sako ‘Yan kungiyar ta Pussy Riot.  

Talla

Ta yi wannan kira ne a wani taro da kungiyar nan ta kasa da kasa mai kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta shirya.

A watan da ya gabata wata kotu a Moscow ta yankewa ‘Yan kungiyar hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyu domin samunsu da aka yi da laifin tunzura mutane da su bijirewa gwamnatin Vladimir Putin, a wata wakarsu ta addini da su ka gabatar a wata majami’a.

A lokacin da aka tambayi Suu Kyi ko bata ganin gwamnatin kasar Rasha za ta zarge ta da cewa da gwamnatin Putin ta ke yi, sai Suu Kyi ta ce ya kamata ita kasar Rasha ta iya daukan gyara idan aka yi mata.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI