Faransa

Fabius ya yaba da matakin tura dakarun ECOWAS zuwa Mali

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Laurent Fabius, ya yaba da matakin da kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, wato ECOWAS ta dauka, na tura dakaru zuwa Mali, inda ya ce, matakin na samun goyan bayan kasar.

Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Laurent Fabius
Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Laurent Fabius
Talla

Ministan ya shaidawa manema labarai a New York cewar, Faransa zata bada taimakon kayan aiki, amma sojojin ta ba zasu shiga aikin ba.

Fabius yace matsalar ta ‘Yan Afrika ce, saboda haka su zasu magance ta.

A dai jiya ne kasar ta Mali ta nemi kungiyar ECOWAS da ta tura dakarunta zuwa kasar ta Mali, domin a taimaka was kasar ta kwato yankin Arewacin kasar da ke hanun ‘Yan tawayen kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI