Rasha

Wani direba ya kashe Marayu biyar a Rasha

‘Yan sanda a kasar Rasha, sun cafke Direban da ya kashe mutane bakwai cikinsu har da marayu biyar bayan motarsa ta abka cikin wani gidan yara, a yayin da ya ke buge da barasa. Shekarun yaran da su ka mutu ‘yan tsakanin shekaru 15 ne zuwa 17 tare da Malamarsu da mijinta, a yayin da wasu masu wucewa su biyu su ka sami raunuka.  

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin 路透社
Talla

A yanzu haka ‘Yan sandan, sun shigar da kara, inda za a tuhumi, Alexander Maximov, da laifin yin kisa da tuki a yayin daya ke buge da barasa.

A cewar Jam’iya mai mulki a kasar za ta shigar da bukatar fitar da tsauraran hukunci ga masu tuki a yayin da su ke buge da giya a gaban majalisar kasar.
 

Mai Magana da yawun, shugaban kasar Rasha, Dmitry Peskov, ya fadawa Kamfanin Dillancin labarai na RIA Novosti a kasar Rasha, cewa yana goyon bayan bukatar a fitar da tsauraran hukunci ga masu tuki bayan sun sha giya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI