Faransa

Hollande ya yi kiran kawo karshen mulkin Bashar al- Assad

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande REUTERS/Mike Segar

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande, yayi kiran kawo karshen mulkin shugaba Bashar al Assad na Syria, saboda yadda yake cigaba da kashe mutanen kasar. Yayin da yake jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya, shugaban ya kuma bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta taimakawa yan gudun hijirar kasar.  

Talla

“Babu yadda za’ayi gwamnatin Syria ta samu wurin zama a cikin kasashen duniya, saboda haka, na dauki matsayin amincewa da shugabanin Yan Tawayen Syria, saboda haka ina bukatar Majalisar ta taimakawa wadanna mutane.”

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, a farkon jawabinsa, ya yi kira da ganin an kawo karshen rikicin na Syria domin yana barazanar hargitsa Yankin Gabas ta Tsakiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI