Girka

Za a shiga yajin aikin gamagari a Girka

Wasu masu kin goyon bayan matakan tsuke aljihun gwamnatin Girka
Wasu masu kin goyon bayan matakan tsuke aljihun gwamnatin Girka Reuters/John Gress

Yau ake saran ma’aikata a kasar Girka zasu gudanar da wani yajin aikin gama gari, yayin da Shugabar Hukumar Lamuni ta Duniya, Christine Lagarde, ke gargadin cewar jinkirin da ake samu wajen aiwatar da sauye sauye a kasar, na haifar da rashin kudade.

Talla

Ana sa ran Ma’aikata, Malaman makarantu, Lauyoyi, Matuka jiragen ruwa da wasu kungiyoyi da dama zasu shiga yajin aikin na sa’oi 24.

Yajin aikin dai ana sa ran zai tsayar da duk hada hada cik a kasar, a yayin da aka yi umurni da ‘Yan kasuwanni su rufe shagunansu, koda yake wasu daga cikin masu shaguna sun ce za su bude ganin yadda kasar ke fama da tattalin arziki.

Wanna yajin aiki shine zai zamanto na uku amma ta farko da za ta gwada hadin kan gwamnatin kasar ta Girka.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI