Spain

Dubban mutane sun gudanar da sabuwar zanga zanga a Spain

A lokacin wata zanga zanga a kasar Spain
A lokacin wata zanga zanga a kasar Spain Reuters

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga zanga kusa da Majalisar kasar Spain, a rana ta biyu, bayan hada hadar kasuwanni ta nuna cewar, kasar na bukatar wani sabon tallafi. Masu zanga zangar sun yi ta kiraye kirayen cewar gwamnati tayi murabus, domin ta gaza wajen shawo kan matsalolin kasar. 

Talla

Wani matashi ya bayyana gwamantin da taga baci wanda take ci a matsayin wanda ta fiwa kasar alheri.

A yanzu haka a cikin matakan tsuke aljihun bakin da kasar ke kokarin yi a shekara mai zuwa, har da kara kudin harajin kayan sayarwa da sauransu.

Masana sun ce kasar ta Spain na bukatar ta sake rage kudaden Fansho, matakin da gwamnatin ta ki dauka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.