Rasha

Rasha za ta gabatar da jawabinta akan zargin kera Nukiliyan da Iran ke yi

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Sergei Karpukhin

Wani babban Jami’in kasar Rasha a yau ze gabatar da jawabinsa a babban zauren taron Majalisar Dinkin Duniya, bayan matsin lamba da kasashen duniya ke yiwa Iran da ta yi watsi da yunkurinta na kera makamin Nukiliya. Ministan Harkokin Wajen kasar Rasha, Sergie Lavrov, ne ake sa ran zai gabatar da jawabin, wanda zai mayar da martani ga Ikrarin da kasar Isra’ila ke yi, na cewa Iran na kera makamin Nukuliya da kuma kira da kasashen ke yi na a dauki matakin soji akan Syria. 

Talla

Abokana kasar ta Syria, wanda aka fi sani da Friends of Syria a turance, za su kebe, inda za su samo mafitar yadda za a sa shugaba Bashar Al- Assad ya sauka daga karagar mulki a saukake.

Kasashen Rasha da Sin, sun kasance kasashe biyu a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya, da su ka ki yarda a dauki matakin soji akan kasar Syria.
 

Wannan jawabi na Lavrov  zai zo ne kwana daya bayan, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya gabatar da wani jawabi inda ya ke zargin Iran za ta iya mallakan mamakin Nukiliya nan da shekara daya.

Kasar ta Iran dai ta dade tana musanta wannan zargi da ake mata, inda ta ke cewa za ta yi amfani da shi ne domin samar da wuta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI