Jamus

Tsohon ministan kudin Jamus zai kara da Merkel a zaben 2013 – Rahoto

Jami’iyar a kasar Jamus ta Social Democrats, ta zabi tsohon Ministan Kudin kasar, Peer Steinbrueck, a matsayin Dan takarar da zai fafata da Shugaba, Angela Merkel, a zabe mai zuwa da za a gudanar a 2013, a cewar wani rahoton wata jarida.

Peer Steinbueck zai yi takara da Angela Merkel a zaben 2013
Peer Steinbueck zai yi takara da Angela Merkel a zaben 2013 (Photo : AFP)
Talla

Jaridar wacce, ake kira Bild, ta jiyo labarin ne daga wasu kusoshin, jam’iyar adawar, ta zabi Steinbueck, dan shekaru 65 a zaben da za a gudanar a watan Satumba ko kuma Oktoban shekara 2013.

Ta kara da cewa, Shugaban jam’iyar, Sigmar Gabriel, zai nema a ba wa Steinbrueck damar wakiltar jam’iyar a wani taro na musamman da za a shirya nan gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI