Faransa

Dubban mutane sun gudanar da zanga zanga nuna Paris akan matakan tsuke aljihu

Zanga zangar nuna adawa akan matakan tsuke bakin aljihu a Paris
Zanga zangar nuna adawa akan matakan tsuke bakin aljihu a Paris REUTERS/Christian Hartmann

Dubban mutane ne a jiya Lahadi a birnin Paris na kasar Fransa suka gudanar da wata zanga zangar nuna adawa da daukar matakan tsuke bakin aljihu a Nahiyar Turai . A cewar jam’iyar nan mai ra’ayin rikau a Faransa ta Front de Gauche, sama da mutane dubu 800 ne suka halarci zanga zangar ta jiya. 

Talla

zanga zangar dai na nufin cewa, daga yanzu al’ummar Faransa sun shiga cikin jerin zanga zangogin da al’ummar Nahiyar Turai ke gudanarwa ne, na nuna rashin amincewa da matakan tsuke bakin aljihun da gwamnaticinsu ke yi a matsayin hanyar magance matsalar tattalin arzikin da suke fuskanta.

Tsohon dan takarar shugabancin kasar Faransa a karkashin jam’iyar ta Front Populaire Jean-Luc Mélenchon da ya halarci zanga zangar tare da wasu ‘Yan majalisun dokokin kungiyar tarayyar turai masu tsatsauran ra’ayi ya bayyana cewa, zanga zangar ta jiya bata da alaka da adawa ga gwamnatin Faransa, inda ya kara da cewa, zanga zangar ta nuna adawa ce ga siyasar tsuke bakin aljihu a Nahiyar Turai.

Baya ga jam’iyar ta Front de Gauche, kungiyoyin kwadago da na fararen hula a Faransa duk sun yi kira ga magoya baynsu da su shiga zanga zangar ta jiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI