Turkiya

Za a tono gawar tsohon shugaban kasar Turkiya

Tsohon shugaban kasar Turkiya Turgut Ozal
Tsohon shugaban kasar Turkiya Turgut Ozal www.news.az

Za a tono gawar tsohon shugaban kasar Turkiya, Turgut Ozal, bayan wani Mai shigar da kara ya bada umurnin yin hakan domin zargin da ake yi ko kashe shi aka yi. Rahotanni sun nuna cewa tuni masu tono kabarin, tare da kwararru da kuma wakilan masu shigar da kara sun bayyana a gaban kabarin, inda aka binne Ozal shekaru 19 da su ka gabata.  

Talla

Bayan mutuwar, Ozal ‘Yan uwa da iyalai da kuma abokanai sun yi zargin cewa an saka mai guba ne a abinci, wanda a yanzu haka kwararru za su tantance ko gaskiya ne.

Ozal wanda shi ne shugaban kasar Turkiya na takwas ya mutu ne a shekarar 1993 a asibiti bayan fama daya yi da ciwon zuciya, inda ya mutu daga baya yana dan shekaru 65.

Alokacin da ya ke Firaministan a shekarar 1988, Ozal ya tsallake rijiya da baya, bayan wani dan bindiga ya nemi halaka shi, amma bai yi nasara ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI