Faransa-Euro

Faransa ta amince da bukatar Turai akan rage gibin kasafin kudi

Shugaban kasar Faransa  François Hollande.
Shugaban kasar Faransa François Hollande. REUTERS/Philippe Wojazer

Kasar Faransa, ta amince da bukatar kungiyar tarayyar Turai ta rage gibin kasashe masu fama da kangin bashi zuwa kashi 0.5 wanda zai kasance a hukumance.‘Yan majalisar dattawa 306 ne suka jefa kuri’ar amincewa da Daftarin kudurin Dokar da aka gabatar a zauren majalisar, a yayin da 32 suka hau Kujerar na-ki.

Talla

An dai gabatar da Daftarin kudurin Dokar ne da gagarumin rinjaye a majalisar, duk da yawan masu adawa da batun, da kuma ke shan suka a wurinsu.

Dama dai majalisar gwamnatin shugaba François Hollande tana cike da goyon bayan Daftarin, da mutane da dama a kasar ta Faransa suke nuna kyama.

Amma a kokarin kara kambama kimar shugaba François Hollande, a cikin gida da waje, mafi yawancin ‘yan majalisar, sun amince da shi, abinda ya bai wa shugaban damar yin gaban kansa.

Sai dai kamin rattaba hannu ga Daftarin ‘yan adawa daga kusa da nesa da bangaren Jean Luc Melenchon zuwa Marine Le Pen, sun gabatar da korafinsu, tare da bukatar a sake dubawa.

Rattaba hannu ga Daftarin dai dole ne ya kasance ya samu amincewar 12 daga cikin kasashe masu amfani da kudin Euro 17 kamin ya soma aiki a shekara mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.