Jamus-EU

‘Yan adawar Jamus sun zargi Merkel game da rikicin Bankunan Turai

Peer Steinbrück Babban mai adawa da Merkel a kasar Jamus
Peer Steinbrück Babban mai adawa da Merkel a kasar Jamus (Photo : AFP)

Abokin hamayyar Shugabar Gwamnatin Jamus, a zaben da za a yi a badi, ya zarge ta da jinkirta samar da matakan da za su bayar da damar saka ido akan harkokin Bankunan Kasashen Nahiyar Turai, inda ya ce, tana yin hakan ne domin cim ma burinta na siyasa.

Talla

Shugaban Jam’iyyar Social Democrats, Peer Steinbruck ne ya yi zargin inda ya ce Angela Merkel na son ta karkatar da batun kafa matakan da za su saka ido akan Bankunan Tarayyar Nahiyar Turan ne, bayan an kammala zaben da za a yi a watan Satumba ko Oktoban badi.

A wani taro da kungiyar Tarayyar Turai ta yi a makon daya gabata, shugabannin Nahiyar, suka amince da daukar matakin kawo karshen matsalar tabarbarewar tattalin arzikin yankin da ke amfani da kudin Euro.

Inda suka jaddada cewa, hakan zai dinga taimaka wa wajen saka ido akan bankunan yankin, wanda hakan zai ba da damar ba su tallafi.

Shugabannin Nahiyar sun amince da a yi hakan ne, a shekara mai zuwa, kamar yadda kasar Faransa ke so.

Sai dai Steinbruek, wanda zai kara da Merkel a zabe mai zuwa, bai amince da hakan ba, inda ya nuna daukar matakan da za su bai wa bankunan Nahiyar damar samarwa kansu kudaden tallafi ba tare da wani ya tallafa musu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.