Jamus

Yawan marasa aikin yi a Jamus ya karu a watan Oktoba

Shugabar kasar Jamus Angela Merkel
Shugabar kasar Jamus Angela Merkel REUTERS/Christian Hartmann

Yawan marasa aikin yi a kasar Jamus ya karu a watan Oktoba, inda ake hasashen hakan bai rasa nasaba da alamu da kafafen samar da aikin yi ke yi na ci gaba da fuskantar koma baya, sakamakon matsalar bashin da ta yi wa kasashe masu amfani EURO katutu. 

Talla

Alkaluman da hukumar kwadagon kasar ta Jamus ta fitar su nuna cewa, a jumulance rashin aiki a watan Oktoba bai karu a kan abin da ake da shi a watan Satumba ba, amma kuma in aka kalli watannin daban daban, wannan watan ya sami karuwa da daga kashi 6.5 zuwa kashi 6. 9.

Rashin aikin ya karu da dubu 20, a daidai lokacin da ake ci gaba da jin illar matsalar tattalin arzikin da Nahiyar Turai ke fama da shi, a kasarta Jamus, da ita ta fi kowacce kasa arziki a tsakanin kasashe masu amfani da kudin EURO.
 

Sai dai Shugaban hukumar kwadagon, Frank Weise, ya ce duk da wadannan matsalolin, tattalin arzikin kasar na samun ci gaba, sai dai ba da yawa ba.
 

Ya kara da cewa zai yi wuya jamus ta kaucewa matsalar da tattalin arzikin turai ke fuskanta, a karshen shekara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI