Birtaniya

‘Yan Majalisar Birtaniya sun ki amincewa da bukatar Cameron

Firaministan Birtaniya David Cameron
Firaministan Birtaniya David Cameron REUTERS/Darren Staples

Yan Majalisar Birtaniya sun kada kuri’ar amincewa da shirin rage gibin kasafin kudin kungiyar kasashen Turai, sabanin bukatar Firaminista, David Cameron wanda ke adawa da shirin. Wasu daga cikin ‘Yan Jam’iyar Firaministan, sun bijire masa, inda suka hada kai da ‘Yan Jam’iyar Labour mai adawa, domin amincewa da shirin na kungiyar kasashen Turai.

Talla

An dai tafka mahawara mai zafi kafin amincewa da kudirin, inda David Cameron yace zai hau kujerar naki idan bai gamsu da manufofin taron shugabanin kungiyar kasashen Turan a makon gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI