Isa ga babban shafi
Birtaniya

‘Yan Majalisun Birtaniya sun nemi Cameron ya kauracewa taron Commonwealth a Sri Lanka

Firaministan Birtaniya David, Cameron
Firaministan Birtaniya David, Cameron Reuters
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

‘Yan Majalisun Britaniya, sun bukaci Firaministan kasar, David Cameron, da ya kauracewa taron kungiyar kasashe renon Ingila da za’a yi a kasar Sri Lanka, saboda yadda kasar ke cin zarafin Bil Adama.

Talla

Kwamitin Majalisar da ke kula da harkokin waje, yace kuskure ne a bar kasar Sri Lanka ta dauki nauyin taron, ganin yadda ta ke ci gaba da kashe fararen hula a cikin kasarta.

Tuni dai Firaministan Canada, Stephen Harper yace shi ba zai halarci taron ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.