Jamus

Netanyahu da Merkel sun sami banbancin ra’ayi akan sabbin matsugunin Yahudawa

Firaministan Isra'ila, Bnejamin Netanyahu (hagu) da Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel (dama)
Firaministan Isra'ila, Bnejamin Netanyahu (hagu) da Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel (dama) AFP PHOTO / JOHANNES EISELE

Firaministan kasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu da Shugabar kasar Jamus sun sami sabani akan batun sabbin matsugunan Yahudawa da ake ginawa a yankin Gaza.

Talla

Merkel, a lokacin da ta ke ganawa da manema labarai, ta bi sahun sauran takwarorinta na Nahiyar Turai, inda ta nuna bukatar Isra’ila da ta dakatar da gina matsugunan Yahudawa guda 3,000 da take kokarin yi a yankin Gaza.

“A game da batun gina matsuguni, bamu amince da hakan ba.” Inji Merkel

Sai dai Netanyahu ya ce sabbin ginaginen da za a yi, shiri na tsoffin gwamnatoci da suka gushe a gaba, inda ya kara da cewa har yanzu yana mutunta shirin da aka yi.

“Sam ban canja wannan tsari ba, wannan tsoffin tsare-tsare ne.” Inji Netanyahu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.