Turai

Bankin Nahiyar Turai ya yi hasashen bunkasar tattalin arziki yankin

Tambarin Babban Bankin Nahiyar Turai
Tambarin Babban Bankin Nahiyar Turai Reuters/Ralph Orlowski

Babban Bankin Nahiyar Turai ya yi hasashen samun raguwar hauhawar farashi kayyaki, tare da samun bunkasuwar tattalin arziki a nahiyar a 2013. Bankin na turan dake da cibiya a Fankfurth na kasar Jamus ya bayyana cewa, za’a samu saukar farashin da 1.6% a yayin da a yanzu yake 1.9% a wannan shekara ta 2012. Bankin har ila yau yayi fatan ganin farashin zai sauka da 1.4% nan da 2014.  

Talla

Har ila yau ta fanin bunkasar tattalin arziki kuma, Bankin na Nahiyar Turai ya bayyana cewa ana da kyawun fatan ganin  a shekarar 2013 tattalin arzikin yankin na turai zai kara cirawa sama daka 0.3% zuwa 0.5% a yayin da a 2014 zai kai 12%.
 

Ita ma kasar Faransa tabakin Ministan tattalin arzikinta, Pierre Moscovici, ya ce suna hasashen Faransar zata samu karin ci gaban tattalin arziki da 0.8% ta yiwu kuma a samu kasa da haka.
 

Salon Siyasar farfado da bankuna turai ta yi muni sosai a kasashen kudancin nahiyar, wadanda matsalar ta tattalin arzikin ta fi yiwa illa sakamakon dimbin basukan da suka hada suka kasa biya, kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.